Tinubu Ba Zai Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda Ba — Bwala
[ad_1]
Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan Tsare-tsaren Manufofi, Daniel Bwala, ya nanata cewa gwamnatin tarayya da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta “ba za ta yi sulhu da ‘yan ta’adda ba”, yana mai sake jaddada matsayin gwamnati na rashin lamuntar duk wani nau’in ta’addanci.
Bwala ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, inda ya bayyana kuskuren gwamnatin baya kan tattaunawa da ‘yan bindiga in hakan shi ne mafita ta ƙarshe.
Sai dai ya ce, duk da cewa, doka ta amince a yi sulhu da ‘yan ta’adda don ceton rayuka, “amma, gwamnatin tarayya ba ta yi sulhu da su ba kuma ba za ta yi ba.”
A cewarsa, gwamnatocin da suka gabata kan yi amfani da tattaunawa a cikin mawuyacin hali inda rayukan ‘yan kasa ke cikin hatsari.
Duk da haka, ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya sauya wannan hanyar, inda ya ce, ba zai tattauna da ‘yan ta’adda ba.
A cewarsa, sauyin manufofin ya samo asali ne, bayan gano cewa, biyan kudin fansa ko rangwame a kaikaice galibi yana ƙara ƙarfafa ‘yan ta’adda ne kawai su ƙara lalubo wasu sabbin hanyoyi
[ad_2]
Source link