Ban Yarda A Yi Maulidina Ba – Wasiyyar Sheikh Dahiru Bauchi

[ad_1]


Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana a cikin wasiyyarsa cewa bai amince a ware ranar 2 ga watan Muharram domin yin Maulidin tunawa da haihuwarsa bayan rasuwarsa ba. Ya ce bai kai matsayin da za a gudanar da taron maulidi na musamman gare shi ba, kamar yadda ake yi wa Manzon Allah (SAW) da wasu fitattun manyan mashahuran Darikar Tijjaniyya.

A cikin bayaninsa, marigayin ya ce shi Muƙaddami ne kawai daga cikin Muƙaddaman Shehu Tijjaniyya, kuma wannan matsayin ya isa alfahari gare shi. Ya bayyana cewa idan har za a rika gudanar da Maulidi ga kowanne Muƙaddami, to babu ranar da ba za a samu taron Maulidi a Nijeriya ba saboda yawan Muƙaddaman da ake da su a Darikar.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi gargaɗi cewa ba ya so a sake danganta watan Muharram da haihuwarsa ko kuma a sanya sunansa cikin waɗanda ake yi wa maulidi bayan rasuwa. Ya ce bai amince ba a faɗa kalaman da ke nuna Muharram ya zo da shi kamar yadda ake cewa Rabi’ul Awwal ya zo da Manzon Allah (SAW), Safar da Shehu Tijjani, da Rajab da Shehu Ibrahim Inyas ba.

Ya nanata cewa a lokacin rayuwarsa, shi ne ya fara gudanar da Maulidin tunawa da Shehu Ibrahim a watan Rajab, amma bai yarda a maida lamari irin wannan na tunawa da haihuwar mutum zuwa ga kansa ba. Ya roƙi almajiransa da masoyansa su bar shi kamar sauran Muƙaddaman Shehu, ba tare da ƙirƙiro masa ranar Maulidi ba bayan mutuwarsa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *