Za a aurar da marayu 200 a Zamfara
[ad_1]
Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu.
Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau.
Ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga mutanen da suka fi buƙatar taimako na haƙiƙa.
Sakataren ya ƙara da cewa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin taimaka musu su fara sabuwar rayuwarsu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link