Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal

[ad_1]



Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao.

Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta.

Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani da shi domin buga wasanni.

Yamal, mai shekara 18, ya buga wasa ɗaya ne kacal a Camp Nou kafin a rufe shi a watan Agusta 2023, inda a yanzu ya ce yana fatan farantawa dubban magoya baya kulob ɗin a sabon filin da aka sauyawa fasali.

A wani saƙo da ya wallafa a Instagram, Yamal ya saka hotonsa riƙe da bajon Barcelona tare da rubutun cewa Camp Nou shi ne wajen da za a rubuta tarihi.

A farkon watan Nuwamba an gudanar da gwajin farkon shigar tara a filin, inda aka bai wa magoya baya 23,000 damar shiga. Sai a yanzu da aka ƙara yawan kujeru domin ɗaukar ‘yan kallo har 45,401.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *