Kofin Duniya 2026 Zai Zama Na Ƙarshe A Wuri Na
[ad_1]
Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta kasar Portugal kuma tauraron kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa, gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026 mai zuwa za ta kasance gasar kofin Duniya na karshe da zai Buga.
Ronaldo ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a wani dandalin tattaunawa a Saudiyya.
Dan wasan gaban mai shekaru 40, wanda ya zura kwallaye sama da 950 ga kungiyoyi da kasa, ya ce yana shirin yin ritaya daga kwallon kafa nan da “shekara daya ko biyu.”, lokacin da aka tambaye shi ko 2026 za ta zama gasar cin kofin duniya na karshe da zai buga, Ronaldo yace “Eh tabbas zan cika shekaru 41 kuma ina tsammanin lokacin ya yi.”
A shekarar 2023, Ronaldo, wanda ke taka Leda tare da Al Nassr ta Saudiyya, ya tabbatar da maganar da ya yi na cewa, zai rataye takalminsa nan ba da jimawa ba, “Idan ina nufin nan ba da jimawa ba, watakila shekara daya ko biyu zan ci gaba da kasancewa a wasan,” in ji shi.
Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar yana da burin buga Kofin Duniya na shida a shekara mai zuwa, ya kusa lashe kofin a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta sha kashi a hannun Faransa a wasan kusa da na karshe, a halin yanzu, Portugal ba ta sami gurbi a gasar 2026 ba, wadda za ta gudana a Amurka, Kanada, da Mexico, amma za su iya samun gurbin shiga gasar ta hanyar doke Ireland a ranar Alhamis.
[ad_2]
Source link