An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

[ad_1]


A yau Asabar ne aka gudanar da wani babban taro na cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin a Beijing, inda shugaban kwamitin kasa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) Wang Huning ya yi kira ga al’ummar kasar Sin a gida da waje da su kara hada kai sosai, su tuna da tarihi da kuma kare nasarorin da aka samu a yakin turjiyar da al’ummar kasar Sin suka yi da zaluncin kasar Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya.

Wang ya yi nuni da cewa, nasarar yakin da kuma maido da Taiwan zuwa kasar Sin manyan nasarori ne ga dukkan al’ummar kasar Sin, kana wani abin alfahari ne na al’ummar kasar bai-daya.

Wang ya kara da cewa, kebe ranar tunawa da maido da Taiwan kasar Sin ya nuna irin jajircewar dukkan kabilun kasar Sin wajen kare ka’idar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma kare ikon mallakar kasa da kuma cikakken ‘yancin yankin kasar.

Kazalika, ya ce, hakan ya kara karfafa fahimta da matsayar da kasashen duniya suka cimma kan cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya farraka shi da kasar ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *