An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya




An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11.

Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun Zariya, ya kai ƙorafi ofishin Rundunar Sibil Difens da ke shiyyar Zariya inda ya zargi malamai na makarantar da laifin.

Wakilinmu ya ruwaito waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Atiyebi Eunice Temitope (da ake kira Misis Okasha) mazauniyar Dogon Bauchi a ƙaramar hukumar Sabon Gari, da Adeyemo Damilola, mazauniyar Hanwa New Extension Zariya, da kuma wasu uku da suka tsere.

A cewar rahoton, matar mai ƙorafin ce ta fara lura da al’amarin yayin da take yi wa yarinyar wanka, inda ta ga alamar an taɓa mutuncinta, inda bayan tambayar yarinyar ta shaida mata cewa malaman sun fara aikata hakan tun tana aji uku a firamare, a shekarar 2023.

Rahoton ya ce, yarinyar ta zargi Temitope da kai ta banɗaki na makarantar har sau uku, inda ta yi mata barazanar kira masu garkuwa da mutane idan ta tona asirin abin da ke faruwa.

Haka kuma, a ranar 16 ga watan Satumba, bayan dawowa daga hutu, yarinyar ta ce Adeyemo Damilola ta kira ta zuwa bene na sashen sakandare, inda ta yi amfani da wani abu kamar sirinji a cikin al’aurarta.

Alƙaliyar kotun, Rabi Hashim, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Oktoba domin samun shawarar ma’aikatar shari’a. Ta kuma bayar da umarnin a tura waɗanda ake tuhuma gidan gyaran hali.

Da Aminiya ta je makarantar domin neman ƙarin bayani, shugaban makarantar, Mista Apoju Sunday Adeyemi, ya tabbatar da faruwar zargin, sai dai ya bayyana cewa har yanzu ana gudanar da bincike, don haka ba zai yi tsokaci sosai kan abin da yake gaban kotu ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *