DSS ta warware tankiyar da ke tsakanin NUPENG da Dangote

[ad_1]



Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar warware tankiyar da ke tsakanin Matatar Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG).

Wannan na zuwa ne bayan wani zama da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, inda rahotanni ke cewa shugabannin NUPENG sun umurci mambobinsu da su dakatar da yajin aikin da aka fara a faɗin ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Kwadago da Ayyuka, Mohammed Maigari Dingyadi; da Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, duk sun halarci zaman.

Haka zalika, tawagar Kamfanin Dangote ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sayyu Dantata ta halarci taron.

Daga cikin shugabannin ƙwadago da suka halarta akwai Mista Akpouha Williams na NUPENG, Mitsa Benson Upah na Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), da Dokta NA Toro na TUC.

A jiya Litinin ce aka tashi baram-baram a wajen taron tattunawar sulhu da aka yi tsakanin ƙunyiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da kuma wakilan kamfanin Dangote.

Kungiyar NUPENG ce ta fusata a sakamakon matakin da Matatar Dangote ta dauka na fara jigilar mai zuwa gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

NUPENG ta ce muddin matatar mai ta Dangote ta fara jigilar mai zuwa gidajen man da ke jihohi, to dubban ma’aikatan da ke aiki a daffo-daffo da kuma direbobin da ke tuƙa manyan motoci sama da dubu 30, za su rasa aikinsu.

Ita ma ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas NOGASA, ta nuna goyon bayanta a kan matakin da NUPENG din ta ce za ta ɗauka na shiga yajin aiki.

To sai dai kuma ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta Arewacin Najeriya wato AROGMA ta ce tana maraba da matakin da Matatar Ɗangote ta ɗauka na yin dakon mai zuwa gidajen man a faɗin ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *