Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu a Sakkwato

[ad_1]



Matasan Ƙaramar hukumar Shagari sun kashe wasu ’yan bindiga shidda da ake zargin suna cikin waɗanda suka addabi yankin Ƙaramar hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Wani matashi ya yi wa wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru ya ce, ’yan bindigar sun zo kan Jakuna a cikin dajin da ba kowa, a safiyar Alhamis inda  mutane da ke tsare gari ba su watse ba suka gansu a nan ne suka yi masu ƙofar raggo, suna tare da shanun da suka sata da wasu baƙin shanu.

“An gansu su bakwai an kashe shidda daga cikinsu an bar guda raye aka ɗaure shi,  su shiddan ga su a kwance ba rai, mutane sun yanke hukuncin kare kansu don sun ga gwamnatin Sakkwato ba da gaske take kan lamarin tsaro ba.” A cewarsu

Shugaban Ƙaramar hukumar Shagari, Alhaji Muhammad Maidawa ya ce da safiyar Alhamis labari ya zo masa akwai wasu baƙin Fulani jajaye da aka afkawa a garin Shagari, amma komai ya lafa sojoji sun kwantar da tarzomar.

Kan maganar adadin waɗanda aka kashe ya ce har yanzu jami’an tsaro ba su gama tantancewa ba, in sun ƙare za su sanar da shi ya ba da bayani.

Matasa a ƙarƙashin Ƙungiyar Shagari Youths a Ƙaramar hukumar Shagari ta jihar sun yi barazanar ɗaukar matakin kare kansu sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Matasan sun kuma zargi gwamnati da sakaci duk da hare-haren ’yan bindiga da ake ta fama da su tare da ƙorafe-ƙorafen jama’a.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Ƙungiyar ta hannun Bello Bala Shagari, ya bayyana cewa matasan sun yanke wannan shawara ne a wani taro na intanet da suka gudanar ranar Laraba.

Ya ce: “Da dama sun bayyana cewa, gwamnati ta gaza wajen cika alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Saboda haka, kare kai yanzu shi ne kaɗai zaɓin da ya rage.”

Ya ƙara da cewa, matasan sun yanke shawarar ɗaukar duk wani mataki da ya dace domin kare kansu daga cin zarafi da hare-haren ’yan bindiga.

Sai dai Shagari ya bayyana cewa, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo/Shagari, Umar Yusuf-Yabo, ya yi kira da a yi haƙuri, a bi doka tare da samun ƙarin shawarwari.

Duk da ya nuna fahimtar takaicin da matasan ke ciki, ya roƙi gwamnati da ta hanzarta ɗaukar mataki domin daƙile abin da ya ce na iya “rikiɗewa zuwa barazana mai girma.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *