Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Yobe ta kwashe magidanta sama da 250 daga Garin Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Nangere, zuwa sabon matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta lalata musu gidaje.

An ƙaddamar da sabon matsugunin ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni domin kare rayukan waɗanda abin ya shafa.

Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (YOSEMA), Alhaji Idi Jidawa, ya bayyana cewa an gina gidajen wucin gadi guda 22 domin amfanin mutanen.

Haka kuma, an samar da rijiya, banɗakunan wucin gadi guda biyar, da motar ɗaukar marasa lafiya.

Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da jami’an Sibil Difens na tabbatar da tsaron jama’a a wajen.

Waɗanda suka samu rauni kuma an tura su zuwa Babban Asibitin Nangere don samun kulawa.

Magidantan da ambaliyar ta shafa sun samu kayan abinci, inda gwamnatin ke shirin ƙara ba su wani tallafi.

Jidawa, ya ƙara da cewa gwamna Buni na da niyyar ganin duk wanda aka raba da gidansa ya koma cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma gode wa Sarkin Tikau, ƙaramar hukumar Nangere, ma’aikatar lafiya, RUWASA, jami’an tsaro, da saurasu wajen ganin an cimma wannan nasara.

Hukumar YOSEMA ta roƙi masu hannu da shuni da ƙungiyoyin agaji da su ci gaba da tallafa wa wannan shiri na taimakon gaggawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *