ASUU Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana Hudu Kan Sabon Tsarin Albashi

[ad_1]

Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwana hudu, inda take bukatar ba tare da bata wani lokaci ba ta far amfani da sabon tsarin albashin da aka amaince da shi ga Malaman Jami’oi a fadin tarayyar Nijeriya.

Shugaban kungiyar, Christopher Piwun shi ne ya bayyana hakan ranar Alhamis ta makon da ya gabata lokacin da yake gabatar da lacca a Jami’ar Sa’adu Zungur,a wani sashen ta da yake Yuli a Bauchi.

  • Kwararru Sun Ankarar Da Manoma Kan Tunkarar Noman Kakar Bana
  • Manufar Sin Ta Yafe Harajin Kwastam Ga Afirka: Alfanun Abin Ya Zarce Batun Cinikayya

Kamar yadda Piwuna ya ce, kungiyar ta ba gwamnatin kwana hudu ne daga ranar ta fara biyan sabon tsarin albashin da aka amince da shi, da aka amince da shit un farko bayan lokaci mai tsawo da aka dauka ana tattaunawa kan lamarin tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar Malamam Jami’oi.

Ya kara jaddada cewa“Mun ba gwamnatin tarayya wa’adin kwana hudu daga yau ta fara biyan sabon tsarin albashin da aka amince da shi. Idan kuma ta ki to za ta hadu da hushin kungiyar kamar yadda ya ce,’’.

Shugaban kungiyar ya ce bukatar tana daga cikin abubuwan da ake so daga cin kokarin da ake na kyautata jin dadin Malaman Jami’oi, domin ayi maganin ko daukar matakin kawo karshen matsalolin da suke damun su, da suka hada rahin albashi mai tsoka, abinda ya ce haka ya taimaka wajen koma bayan ilimin manyan makarantu a Nijeriya.

Ya ci gaba da bayanin duk da yake an cimma matsaya da gwamnatin dangane da wasu yarjejeniyoyi,a shekarun da suka gabata, sai dai kuma aiwatar da su shi ne abin ya zama tamkar wani kadangaren bakin tulu, hakan shi yasa ake ta ci gaba da samun matsaloli sanadiyar rashin aiwatarwa tsakanin gwamnatin da kungiyra ta Malaman Jami’oi.

Masu lura ko nazarin yadda lamurra suke sun ce wa’adin da kungiyar Malaman ta bada na iya sa gwamnatin ta shiga taitayin ta,wasu na ganin idan hakar ta Malaman ba ta cimma ruwa ba, na iya kasancewa tafiya wasu yaje- yajen aikin a Jami’oin gwamnati, matukar ba, a samu biya masu bukatar ba a cikin wa’adin kwanakin da suka bada.

Kungiyar ASUU tana da tarihin tafiya yaje- yajen aiki domin su matsa a biya mata bukatun ta, matakan da sau da yawa ko mafi akasari suna kawo cikas kan lamurran da suka shafi karatu a fadin tarayyar Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *