’Yan Najeriya na cikin manyan masu zubar da abinci a duniya




Shirin Abinci ta Duniya (WFP) ta bayyana cewa ana zubar da kusan tan biliyan 1.3 na abinci a duniya duk shekara.

Rahoton na nufin ana zubar da kusan kashi ɗaya cikin uku na abincin da ake samarwa a duniya a duk shekara.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da miliyoyin mutane ke fama da yunwa, ciki har da ’yan Najeriya da ke fuskantar tsadar rayuwa da wahalar samun abinci.

Rahoton WFP ya nuna cewa mutum ɗaya na zubar da kusan kilo 170 na abinci a shekara, yayin da sama da mutane miliyan 295 a duniya ke fama da matsananciyar yunwa.

Ana danganta asarar abinci da matsalolin adanawa da sufuri, da kuma sayen abinci fiye da abin da mutum ke buƙata.

Masana na cewa idan aka rage ɓarnar abinci, hakan na iya taimakawa wajen rage yunwa da tsadar rayuwa a ƙasashe kamar Najeriya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *