Trump ya bai wa Iran wa’adin sa’o’i 48 ta buɗe Mashigar Hormuz
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Iran wa’adin sa’o’i 48 ta buɗe Mashigar Hormuz domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa, ko kuma ta fuskanci munanan hare-hare kan manyan cibiyoyin makamashinta.
Barazanar ta zo ne a ranar Asabar, a daidai lokacin da Iran ta kai mafi muni cikin hare-harenta zuwa yanzu kan Isra’ila tun bayan fara yaƙin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa Amurka za ta “kai hari tare da rusa” manyan tashoshin makamashin Iran idan har ba a buɗe mashigar ba cikin wa’adin da ya bayar.
Sai dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsu ta taƙaita zirga-zirga ne kawai ga jiragen ƙasashen da ke da hannu a hare-haren da ake kai wa Iran, tare da cewa za su ba da kariya ga waɗanda ba su shiga rikicin ba.
Haka kuma, sojojin Iran sun yi barazanar kai hari kan cibiyoyin makamashi da na samar da ruwa na Amurka da ƙawayenta a yankin.
Wannan na zuwa ne bayan wasu makamai masu linzami daga Iran sun afka wa kudancin Isra’ila, inda suka jikkata sama da mutum 100 a garuruwan Arad da Dimona.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani “a dukkan fannoni,” yayin da Isra’ila ta ce hare-haren sun lalata gine-gine da manyan ramuka a ƙasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa Dimona na ɗauke da wata cibiyar nukiliya mai muhimmanci, duk da cewa Isra’ila ba ta taɓa tabbatar da mallakar makaman nukiliya ba.
Iran ta ce harin da ta kai martani ne ga farmakin da aka kai cibiyar nukiliyarta ta Natanz.
A halin yanzu, rikicin ya janyo rufe Mashigar Hormuz, wadda ke ɗaukar kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur na duniya, lamarin da ya haddasa tashin farashin mai inda kawo yanzu nau’in Brent ya haura dala 105 duk ganga.
Iran ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya mafiya arzikin man fetur, sannan take da iko da muhimmayar hanyar jigilar man fetur na yankin Gabas ta Tsakiya, wato mashigar Hormuz.
Kasashe da dama ciki har da Birtaniya, Faransa da Jamus sun yi Allah-wadai da matakin Iran, tare da nuna shirin taimakawa wajen tabbatar da tsaron zirga-zirga a yankin.
Masana na ganin wannan sabon takun saƙa tsakanin bangarorin biyu na iya ƙara tsananta rikicin tare da ke ci gaba da barazana ga tattalin arzikin duniya baki ɗaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link