Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara
[ad_1]
Bayanan haraji na hukumar haraji ta kasar Sin sun bayyana cewa, a watannin Janairu da Fabrairu na wannan shekara, ci gaban fasaha da kimiyya na kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi.
Bayanan sun nuna cewa, a watannin Janairu da Fabrairu, masana’antun kirkire-kirkire na kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri. Kazalika, kudaden shiga na manyan masana’antun kimiya da fasaha na zamani ya karu da kashi 16.1% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kana yana ci gaba da bunkasa cikin sauri. Daga cikinsu, kudaden shiga na manyan ayyukan hidima ya karu da kashi 17.2%, musamman ayyukan dillalan fasaha, da binciken kimiyyar hallitu da gwaje-gwaje, sun karu da kashi 25.6% da 17.4% bi da bi.
Har ila yau, kudaden shiga na manyan masana’antun kere-kere ya karu da kashi 14.5%, sakamakon bunkasar da ake samu daga tattalin arzikin sararin sama kusa da doron kasa, da kasuwancin sararin samaniya, da kayan laturoni, da masana’antun kera jiragen sama, da na’urorin sadarwa na laturori sun karu da kashi 28.5%, da 18.4% bi da bi. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link